Skip to content
Lyric
Dive
Public playlists
My playlists
Search
Sign in
Hadiza
Ali Jita
Popularity ยท Low
+
๐ณ๐ฌ Hausa ยท Original
0
0
YouTube
Searching YouTube...
Lyrics
Original
Translation
Bilingual
Uhm!
Sannu Hadiza, Hadiza sannu baiwar Allah
Karatun boko, akwai karatun Sallah
Ilimi yayi rarin jini yasa kin wala
Nutsa, dubi jikin Khadija bata wahala
Ga mukamai, Allah ya baki dole ki wala
Ga farin hali gun Hadiza bata hasala
Jinin sarakai, Allah ya baki ba wata kila
Mai adon birni ce Khadija na kala da kala
Kwalliya nai miki kyau, Hadiza baiwar Allah
To wai ina mata, sai ku bita ya ta Sarauta
Yar gidan girma ai Hadiza ta cancanta
Yar gidan girma ce Khadija in kun ganta
Ai tana burgewa, Hadiza sa kayanta
Ku tafawa Hadiza Gimbiyar mata
Makaranta a halinta duba yar gata
Sai ku mike, ku biyo ta, kar ku kyale ta
Ga sarauta an bata, ba'a kwace ta
Ga wadata an bata, ba'a raina ta
Ga kirari na Hadiza, nayiwa wakata
Mace ce, amma Gimbiya cikin mata
Sannu yar lele, Rabbana ya inganta
Yau ina waka, ta Hadiza son kowa
Mai kamala, fuskarta gata kyakkyawa
Ga Hadiza tazo, a daina bin kowa
A raka ta, ta zauna, a dinga gaidawa
Hm! Hadiza, Gimbiya Hadiza (nana Hadiza)
Hadiza Sarauniya Hadiza (nan Khadija)
Khadija ga Gimbiya Khadija (nana Hadiza)
Masu fifita sannu kuyita juyawa (nana Khadija)
Masu gadinta guri ku kara kamawa (nana Hadiza)
Khadija ga Gimbiya Khadija (nana Khadija)
Hadiza, hm! Gimbiya Hadiza
Hau kilishinki, Hadiza kiyita runtsawa
Saka sarkanki ta gold, da ba'a saidawa
Dubi takalminki irin na turawa
Ga jaka, da mayafi ki dinga yafewa
Ga kudi sababbi, ki dinga badawa
Hadiza, Gimbiya Hadiza (nana Hadiza)
Hadiza, sarauniya Hadiza (nana khadiza)
Khadija, adon gari Khadija (nana Hadiza)
Khadija sinadari Khadija (nana Khadija)
Khadija, ga tambarin Hadiza (nana Hadiza)
Um! kirari, nake yiwa Khadija (nana Khadija)
Jita tana fadin Khadija
Hm! sarewarki ma duban, Khadija
Hm! rawar girma, tashi ke Khadija
Hm! karshen magana ina Khadija
An buga an kyale ki ne Khadija (nana Khadija)
A gurin zance ma kinada hujja (nana Khadija)
Ya magauta, sukayi dake Khadija (nana Khadija)
Um! kiyi sha'aninki kinga babu danger (nana Khadija)
Khadija, Sarauniya Khadija (nana Khadija)
Hadiza, Sarauniya Hadiza (nana Khadija)
Hadiza, adon gari Hadiza (nana Hadiza)
Khadija, sanadari Hadiza (nana Khadija)
Ku tafa, matan kawai ku tafa
Ku tafa, matan kawai ku tafa
Da jindadi na da kun yi mata (nana Hadiza)
Khadija
Nana Hadiza
Ko a dangi sam ba kamar Hadiza (nana Khadija)
Um Khadija, Gimbiya Hadiza (nana Hadiza)
Khadija Sarauniya Hadiza (nana Khadija)
Ku tafa mata kawai ku tafa (nana Hadiza)
Nana Khadija
ย