Skip to content
Lyric
Dive
Public playlists
My playlists
Search
Sign in
So Mai Sonka
Umar M. Shareef
Popularity ยท Low
+
๐ณ๐ฌ Hausa ยท Original
0
0
YouTube
Searching YouTube...
Lyrics
Original
Translation
Bilingual
So mai son ka
So mai son ka
So mai son ka duniya zance na kuji
Wanda yaki ka barshi haushi sam kar kaji
Ba a so a dole
Yarinya ki kyale
Ni tuni na silale
Duk munin ka wata kai mata kyau hakane
Duk kyawun ki wani bai so ya gano ki ne
Anyi ruwa da iska
Manoma nata shuka
Allah sa tayo albarka
Guntun gatarin ka dauke ki shi ka rataya
Mai yi maka dan kira barshi karda ka waiwaya
Kwantar da hankalin ka
Yi abinda yake gaban ka
Ka amfani lokacin ka
Ba kowa ake fadawa sirri ba na zuciya
Ka lura da harshe kar yasa ayi maka rijiya
Aboki zo fahimta
Zance in zaka furta
Ka tauna kar ka rufta
Hannun ka bazai rube ka yanke ba ka yada shi
Ina mai shawarar ka karo hakuri dashi
Kar da ka sanya naushi
Ka janyo hankalin shi
Kayi wa'azi gare shi
Rike mai son ka a cikin dadi ko wuya
Karda ka yada mai fada ma kayi gaskiya
Gare ka na daga murya
Mai nema je ka shirya
Rago na kira maraya
Karda ka dau batun da baka san asalin sa ba
Akwai labarukan da basu ma inganta ba
Ka sanya ido ka duba
Kayi wa irin su lamba
Kar su hada ka gaba
Kar kayi wa mutum hukunci in baka san shi ba
Kar ka zace shi sharri baka san halinsa ba
Ba kyau haka in ka duba
A sannu dashi ka saba
Komai ka fadi a karba
Ka zam mai hakuri fushi bai zama naka ba
Idon duniya a kan ka yake ko ba haka ba?
In anyi ma ka kyale
Kunne da ido ka kulle
Hanyar kauce ka bulle
Cikin duniya akwai masoyi akwai makiyi
Kowanne akwai kalar nashi da ra'ayi
Zance na babu shayi
Da manzo zanyi koyi
Ku biyo ni kuzam a layi
Abar tsuntsu a sama can ne zai wataya
Kifi yafi son ruwa ciki ya dimulmuya
Damo na son harawa
Kuba yara alawa
Kar kuyi musu rowa
Abinda yake hannun ka damke shi ka martaba
Ba lallai bane kowa ya soka ba
Babu mai maka sai Rabba
Ka roka zaya karba
Mai talla yake da riba
ย