Skip to content
Lyric
Dive
Public playlists
My playlists
Search
Sign in
Kukan Kurchiya
Adam A. Zango
Popularity ยท Low
+
๐ณ๐ฌ Hausa ยท Original
0
0
YouTube
Searching YouTube...
Lyrics
Original
Translation
Bilingual
Gata, gata nan ku
Ku bude kunnayenku
Sam karkuyi shakku
Labari zan baku
ย
Eh, yan uwana yan Najeriya ga kasida duk kuyi bibiya
Zancen yan dauri na binciko, rubutu ne na mazan jiya
Ga hasashe ga zurfin sani, wanda babu batun san zuciya
Duk ku bini a sannu a hankali, wanda bai gane ba ya tambaya
Binciken mu akan Najeriya yana nuna da ba'a shan wuya
Ba kabilanci na hassada komai sai ayi bai daya
A da Najeriya ba fadan adinni ko daya
A da Najeriya ba fadan na siyasa kun jiya
A da Najeriya ba fadan na kabilancin tsiya
Ba ware jinsi ko daya
Ku duba Nnamdi Azikiwe shi da Sardauna duk bai daya
Tafawa Balewa lokacin gwarzon mu daya rike gaskiya
Su rike Najeriya
Hanu biyu, biyu da gaskiya
Sanan sun tausaya
Ko mataulanta bai sha wuya
Bara kuji zancen gaskiya
Wanda kakan mu yayo jiya
Mawakan gaskiya Sa'adu Zungur namu mazan jiya
Zance ne wanda yayo jiya
Gashi a yanzu anai Najeriya
Eh, sai ku dan tsaya ga kasidar yanzu da zan biya
ย
Matukar a Arewa da karuwai yan daudu dasu da magajiya
Ga samari masu ruwan kudi ga mashaya chan a gidan giya
Matukar 'ya'yan mu suna bara a titunan logon Najeriya
Hanyar birni dana kauye Allah baku mu samu abun biya
Sun yafu da fatar bunsuru, babu tanyar da dukiya
Babu shakka yan kudu zasu hau dokin mulkin Najeriya
In kodai har yan kudu suka hau babu sauran dadi sai wuya
Kowa zai sha wuya
Malaman mu kofa zasu sha wuya
Dangi Najeriya
Talakawa har da mai kudi dukanin mu kofa zamu sha wuya
ย
Eh, a Arewa zumunta ta mutu sai karya sai sharholiya
Canfe, canfe da tsubacen, tsubacen malaman karya yan dafara
Sai karya sai kwanbon tsiya
Sai hula mai anakiya
Ga barin asali dana dukiya
Sai kace 'dan annabi fariya
Jahilci yaci lakar mu duk
Yasa mana sarka har wuya
Yasa mana ankwa a hanuwa
Ya daure kafarmu da sarkiya
Bakunan mu yasa takunkumi
Ba zalaka sai sharholiya
Wanga al'umma me zatayo a cikin zarafofin duniya
Hausawa bamu da zuciya zamu sha kunya nan duniya
Mudai aikin mu gaya muku, ko ku karba ko kuyi dariya
Dariyar ku tazam kuka gaba, da nadamar ma kin gaskiya
Gaskiya bata neman ado, ko na zakin muryan zabiya
Karyace mai launi bakwai
Ga fari da baki ga rawaya
Ga kore ga kuma harda shi toka, toka da ja sun gauraya
Manyan Najeriya
Kun ji halin yau da matashiya
Sai ku gyra dan ceton kasa
Yan Arewa muna tsaka mai wuya
Wayyo Najeriya
Ga tarin dukiya
Shugabani nasan zuciya
Jamma'a na faman shan wuya
Kunci kukan kurchiya
Sako ne tun na mazan jiya
Allah ka hada kayukan mu gabaki daya, ameen
ย